KARATUTTUKA na MAJALISIN SUNNAH
00 Introduction
Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhu
The purpose of these brief summaries is to give the reader/listener an insight to the content of each audio so that hopefully they may have intrest in downloading the audio file for learning. Enjoy.
______Post Format___
0000
date
Lesson
Sheikh
▪
▪
▪
_____________size
■
0006
29/08/2016
Karatun Asuba (Fiqhu)
_____Darusa_________
1. _ _ _
▪ Barin sallar Juma'a don gudun cutarwa na azzalumi....
2. _ _ _
▪ Anso gaggauta bude baki da kame harshe daga surutan banza a yayin azumi...
3. _ _ _
▪ Yanka yana da sunnoni....
>> fuskantar da dabba zuwa ga qibla.
4. IBN ASHIR
▪ Ka sanya mayafi da gyauto da silifa sai ka dauki dabban hadaya tare da kai....
5. _ _ _
▪ Babin gusar da najasa da abun da ake afuwa gareshi.
6. _ _ _
Wanda ya sayar da bawa al'hali bawa na da dukiya, dukiyar na mai sayarwa ne.
- - Tambayoyi.
_____________________mp3, 9mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQN2lFX1hXNzNxZ0U/view?usp=drivesdk
■
0007
Karatun Asuba
30/08/2016
Karatun Asuba
___Darusa_______
1. _ _ _
▪ "Lalle mu gare ku masoya ne" yahudawa sunyi qawance ga kafiran makka sai suka saba musu.
2. _ _ _
▪ Tsare mutuncin mutum shine ya bayar da abunda yake rowa da shi.
3. _ _ _
▪ Haqiqa ranan nan na shiriya ya bullo a goshin manzon Allah (saw).
4. _ _ _
▪ Mun gaaji wadaata da daraja kaka da kakanni kafin yaqin karbala.
5. Lugha:
▪ zaki ya tafi neman zaki.
6. Rarrabuwa na fi'ili.
_____________________mp3, 11mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQS0xwSS1sWTB5ak0/view?usp=drivesdk
■
008
06/09/2016
Karatun Lugah
___Darusa_________
1. _ _ _
▪ Jumloli.
2. _ _ _
▪ Fataha da kasara.
3. _ _ _
▪ mafiyan masu halartar majalisi talakawa ne.
4. _ _ _
▪ Farisawa sunyi shirin daukan fansa amma khalid yayi nasara akansu.
_______________________amr, 5.4mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQdFhweUVCNXoySlE/view?usp=drivesdk
■
0009
24/09/2016
Karatun Asuba
___Darusa______
1. _ _ _
▪ Mu'awwiqi na hudu (04)
>> neman kafa da yawan shagulgula.
2. _ _ _
▪ Ya na wajaba ga mamaci wanka da ruwa mai tsarki.
3. _ _ _
▪ Babin farillan azumi.
4. _ _ _
▪ Yana halatta mutum ya ce Suratul Baqara, Suratul Ali-Imran, Suratul Nisa da Suratul Ankabut.
>> babu karhanci akan haka.
___________________mp3, 7.4mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQejVuNHRmOHZPNm8/view?usp=drivesdk
■
0010
25/09/2016
Karatun Manhaji
_____Darusa__________
1. _ _ _
▪ Adduraru bahiyya ⚊ taqadimin sheikh Bashir bn Nuhu Assalafi.
>> Haqiqa al'umma sun rarrabu kamar yadda manzon Allah ya fadi.
2. Jawami'ul Fawa'id ➡
>> Abu hanifa ya sami ilimi ta hanyar mudahara da muzakara a shagon sa.
3. Adabul Mufrad ➡
>> babin falalar mace tayi hakuri da danta bayan mutuwar mijinta.
>> babin tarbiyya na maraya.
___________________mp3, 10mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQWllCM1RkZ1I1SjA/view?usp=drivesdk
■
0011
03/10/2016
Karatun Fiqhu
1. Albidaya fi ilmul mu'ariz ➡ mukhtasaru zaidun.
>> Mutum ne ya mutu ya bar uwa da kaka da yar-uwa shaqiqiya, dan-uwa li-abbi da yar-uwa li-abbai.
Asalin matsala shida(6) ne:
Za'a kasa dukiya kashi sha takwas (18)
Uwa ➡ 1/6 * 18 = 3
Kaka ➡ 1/3 * 15 = 5
yar-uwa shaqiqiya ➡ 1/2 * 18 = 9
dan-uwa li-abbi da yar-uwa li-abbai ➡ za'a raba musu abun da ya rage(1) rabiyan namiji da mace.
2. _ _ _
▪ Sallah;
barin sallah ta hanyar mantuwa ko bacci.
ana umurtan yaro da yayi sallah in ya kai shekara bakwai (7).
______________________mp3, 8.2mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQWVpMcFdiOUFjdDA/view?usp=drivesdk
■
0013
12/01/1438
14/08/2016
Mu'amalatul Hukkam
Peji na 67
____Dalili na biyu_______
>> wajibi ne akan musulmi ji da biyayya ga shugaba ko a cikin quncci ko sauqi na rayuwa sai dai in ya umurce ka da sabawa Allah.
________________mp3, 11.2mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQZWtEZy1ieHBEUUU/view?usp=drivesdk
■
0015
18/10/2016
Karatun Asuba
____Darusa________
1. _ _ _
Waqa'atul Firaz (sham)
>> Khalid bin walid da rundunar sa.
2. _ _ _
▪ Babin bayanin tawye imani da tawye da'a. Dakuma wawaita kalmar kafirci.
--shin mutum ya kafirta idan ya bar sallah?
3. _ _ _
Yanki yanki na jumla.
__________________mp3, 6.1mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQbnMyR1ktcXVLSG8/view?usp=drivesdk
■
0016
19/10/2016
Karatun Asuba
____Darusa________
1. _ _ _
▪Ayyuka da suke kan bawa.
2. _ _ _
▪Rarrabuwan wajibi ta hanyan abun nema.
3. Sarfu:
▪mai illa ga aynun ko lamun.
4. _ _ _
▪Duk abunda ya gabata na sallan manzon Allah (saw), da maza da mata sun yi daidai a cikinsa.
>> bai zo ba a cikin hadithi na abunda ke hukunta ware mata a cikin wannan sashe.
_______________________mp3, 5.7mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQUzRwS1BaNFNOTzg/view?usp=drivesdk
■
0017
24/10/2016
Karatun Asuba
___Darusa_________
1. _ _ _
▪Duk inda aka tunkude haddi, yaro na risqan mutum.
2. _ _ _
▪ Ranstuwa daga barin abu.
3. _ _ _
▪Qabilan Nahad:
Allah ka sanya albarka ga qabilan Nahad, da cikin tsantsan nono, da nono da tsala.
4. Albidaya fi ilmul muwariz:
▪Tis'iliyatu zaidun.
Asalin matsala shida (6) ne saboda yan uwa na dayawa. Za'a raba dukiya kashi sha takwas(18).
▪uwa 1/6 *(18) = 3
▪kaka 1/3 * (15) = 5
▪yar-uwa shaqiq 1/2 (18) = 9
abun da ya rage (1) za'a kasa shi kashi biyar. Maza zasu samu kashi bibbiyu, ita kuma a bata kashi daya.
▪yan - uwa liabb su biyu (2)= 2(2/5)
▪yar - uwa liabb = 1/5
________________________mp3, 5.1mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQaDZHZm5NcGFWVW8/view?usp=drivesdk
■
0018
24/10/2016
Karatun Asuba
_____Darusa_________
1. _ _ _
▪Lallai abu jahal da wanda suke tare da shi sun san manufan manzo (saw).
2._ _ _
▪ Shin mai shi yana tsammanin soyayya na buya ne.
3. _ _ _
▪Ka ga! Ubangijin daukaka ya ba shi(annabi) falala na har abada kuma ya bashi alfarma abun karfafawa.
4. _ _ _
▪Annabi (saw) shine alfaharin musulmai.
5. _ _ _
▪Wasu mutane suka hana su(yahudawa) daga zagin annabi (saw) amma basu hanu na. Sai aka halaka mai umurni na mai hani.
6. _ _ _
▪Ka ga! shi tsoho idan ka miqar da shi daga karkacewarshi ba zai iya miqar wa daga abin da ke karkace shi ba. Haka reshe mai sauqi ne in yana danye kuma zunguranshi yana da tsanani in ya bushe.
_____________________mp3, 6.6mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQTW1hWEdVODlEZms/view?usp=drivesdk
■
0022
24/01/1438
26/10/2016
____Darusa__________
☀ Sharh aqidatissalaf;
Siffofi haqiqa sun tabbata ga Allah, sanannu ne daga littafin Allah kuma da sunnar manzon Allah.
Sheikh Mahmud Gumi yayi matuqar aiki akan littafinsa Raddul Azhar.
Sheikh Ibrahim Inyas ne ya fara qarfafa yin qabalu a cikin sallah a nan Nageriya.
_____________________mp3, 10.6mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQejRJM1hUaE1WOHc/view?usp=drivesdk
0023
06/11/2016
Karatun Asuba
____Darusa__________
1. _ _ _
▪Malamai sun ambaci sunayen kungiyoyi a cikin littafai da dama, amma cewa suna cikin kungiyoyi halakakku sai da hujja
_________ibn Taymiyya.
2. _ _ _
▪Neman ilimi a cikin girma yana yiwuwa. Umar bn khaddab da Suhayl bn Amr sun nemi ilimi a shekaru na manyanta.
3. Aquidatul Wasidiyya
▪Fadin manzon Allah:
"Ya ku mutane ku sassauta muryarku lalle wanda kuke kira ba kurma bane"
4. Aqidatul Dahawiyya
▪Dole ne muyi imani da azabar qabari.
______________mp3, 12.6mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQZ1hRMVpSNHZDc1U/view?usp=drivesdk
■
0026
28/12/2016
Karatun Asuba
1. _ _ _
▪Sabani na biyar (5)
Yana daga cikin mafi girman mushkila wanda ya fuskanci musulunci wato sabani na shugabanci. Haqiqa Mujaahidun da Ansar sunyi sabani akan wannan matsala.
2. Jawami'ul Fawa'id ➡
▪ya kamata ga ma'abocin ilimi kar ya wulaqantar da kanshi da kwadayi acikin abun da be dace ya zama abun kwadayi gareshi.
3._ _ _
▪ Su murji'awa a wajen su imani baya qaruwa kuma baya raguwa. Gaskatawa shine imani a wajen su. Annabawa da sauran mutane suna da imana iri daya a wajen murji'awa.
4._ _ _
▪ Babu shakka lalle matsalolin jihadi da kuma yaqi yana daga cikin zurfafan matsaloli dake buqatan sanin nassoshin Al Qur'ani da Sunnah.
■
0027
19/12/2016
Karatun Asuba (Fiqhu)
_____Darusa___________
1. Qawa'idi ➡
Babin sujada kafin sallama.
2._ _ _
Duk wanda ya manta da sujada guda biyu to ya fadi yayi sujada.
3. Ashmawi ➡
Idan sallah ya kasance ga mace(marigayiya).
4. _ _ _
Itiqafi yana baci da manyan laifuffuka.
5. Ibn Rushud ➡
Abun da basu yi itifaqi gareshi ba to sabanin su yana nasuwa zuwa gareshi.
Yankan wanda ba balagagge ba, ya halatta.
yankan mace ya halatta, banda malikiyya.
6. Ibn Ashir ➡
kayi qasarun azahar da la'asar(a Arafa)....
7. _ _ _
Wajen kulle daki ayi bismillah, hakanan wajen huce wuta, da shiga, da sanya tufafi, da tubewa, da cin abinci, da sanya mamaci cikin qabari, da runce idanuwa, da hawa mimbari, da saduwa da iyali, da hawa abun hawa, da farauta, da yanka da sokewa.
8. Risaalah ➡
qirada ya halatta da dinari da dirhami.
________________________mp3, 11mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQeU9vZTZma3l1S0U/view?usp=drivesdk
■
0028
20/12/2016
Karatun Asuba(Luggah)
___Darusa__________
1. Alburda ➡ halaye na (na son annabi) ya qetare ka, sirri na be zama abun boyuwa ga masu annamimanci ba. Cutana bai zamo abun yankewa ba.
2._ _ _
Sahabbai da alayen manzon Allah sunfi wadanda suka gabace su.
3. _ _ _
Ladan wanda ya dawwama a addinin manzon Allah ya daukaka.
4. Annabi ya zage dantse don lahira sai ya karkatar da ingarman dokin sa don ya gujewa duniya.
5. _ _ _
Daukakanka ya tabbata a cikin ayyukan da'a.
________________________mp3, 6.6mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQekdULWxYbEpMdGM/view?usp=drivesdk
■
0029
21/12/2016
Usulul fiqhu
Musdala'il hadith
____Darusa___________
1. _ _ _
Kalma na 'shatun'(akuya) ana wawaitashi ne ga dabbobin da ba shanu ba, kuma ba raquma ba, na dabbobin gida.
2. _ _ _
Masu qirqiro hadithi: wasu sashe daga cikinsu suna yi ne;
don bata addini.
don kare ra'ayin su.
don sana'a (wato suyi magana mai dadi don kwandala).
3._ _ _
▪Hadithi wanda yake Matruk:
yana kasance wa da sababin tuhuman mai riwaya da qarya.
▪Hadithi Munkari yana kasance wa idan mai riwaya kuskurenshi yayi muni, Rafkanuwanshi yayi yawa, fasiqancin ya bayyana.
___________________________mp3, 8.3mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQTXZtLVFGWFdVbTQ/view?usp=drivesdk
■
0030
21/03/1438
21/12/2016
Aqidatissalaf
Pegi na 114
___Darusa____________
1. "Idan hadithi ya inganta daga manzon Allah (saw) to lalle yana wajaba ayi riqo da wannan hadithi." ___Shafi'i.
"Idan hadithi ya inganta to wannan shine mazhabi na"____Shafi'i.
_______________________mp3, 10.7mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQbXFkNlBsN1p1Q28/view?usp=drivesdk
■
0031
25/12/2016
Karatun Asuba
___Darusa__________
1. Adduraru bahiyya ➡
Sabani na takwas(8): sunyi sabani wajen nadawan da Abubakar(ra) yayi wa Umar(ra).
Sabani na tara: sunyi sabani gameda shura.
2. Jawami'ul Fawa'id ➡
Mu'awwiqi na takwas(8): debe tsammani daga samun ilimi.
3._ _ _
A cikin usulul fiqhi akwai Al-waraqat(na imamul Juwairi) da Raudatul nazil(na ibn qudama).
4. Mujmal ➡
Tabbatar da hikima a cikin ayyuka na Allah.
________________________mp3, 10.7mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQczBST3pYZjVsODg/view?usp=drivesdk
0032
27/12/2016
Karatun Lugah
____Darusa__________
1. Bincike: Majazi Lughawi
2. Harufofi na Qari
3. Rarrabuwan Fi'ili
4. .....kada ya zare hanu daga yi mishi biyayya.
5. ......haqiqa kayi qoqari ka kama tauraro surayya da hanu.
6. Li'irabin abunda ake yiwa li'irabi da wasullah.
_____________________mp3, 8.4mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQQ1JYQUJuOUI4d0U/view?usp=drivesdk
■
0033
29/03/1438
28/13/2016
Sahih Bukhari
Babin sayan bawa daga kafiri 'harbi' da kuma kyautan shi da yancin sa.
_____________________mp3, 11mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQQkVyMjBlY3JWV00/view?usp=drivesdk
■
0034
04/01/2017
Karatun Asuba
___Darusa__________
1. Usulul Fiqhi:
...."kada ku mutu sai kun kasance kuna musulmi."
"kada ku yi baqin ciki akan abunda ya kubuce muku."
2. _ _ _
Misali na biyu: ciyar da dangi, wajibi ne wanda ba'a qaddara ba sai dai in kotu ta hukunta.
3. Sarfu:
Hazzama Hamza.
4. _ _ _
Na uku: "Sharri baya cikin aikin Allah"
5. _ _ _
Ta'arifin Hukunci.
6. _ _ _
Shin umurni yana hukunta maimaita wa?
_________________mp3, 12.7mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQMVJZUmZBalNRSnc/view?usp=drivesdk
■
0035
17/01/2017
Karatun Fiqhu
Sheikh Yahya bn Muhammad
___Darusa_______
1. _ _ _
Babin Azumi: azumin ramadan farilla ne, yana tabbata da cikan sha'aban.
2. Izziyya - Babi na shida gameda aikin hajja: aikin hajji wajibi ne sau daya akan da.
3. _ _ _
Duk wanda aka zare mishi hankali ( me maye, ko me hauka, ko wanda kare ya ciza) yankanshi haramun ne ga itifaqin malamai.
4. Ibn Ashir - ka tsaya kayi addua a mash-alul haram.
5. _ _ _
Babin abubuwan dake warware alwala.
6. _ _ _
Ban ruwa ya halatta ga itatuwa, da biyan mai aiki daga amfanin su.
7. _ _ _
Rabinsa (sadaki) shi yake cancanta da saki. Matar da aka saka ba tareda an take ta ba, ta ci rabin sadaki.
______________________mp3, 7.2mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQcmg3TWxqV3pOTlk/view?usp=drivesdk
■
0036
10/01/2017
Karatun Lugha
___Darusa_______
1. _ _ _
Lallai rai na wanda ke umurnina da mummunan aiki be wa'azantu ba da mai gargadi na furfura mai tsufa saboda jahilcinsa.
2. _ _ _
Duk wasu ayyuka na alkhairi taken manzon Allah ne tsawon zamani.
3. _ _ _
Mashi ya damfàre su.....
4. _ _ _
Duk wanda zamani bai mishi wa'azi ba to malami bai isa ya yi masa wa'azi ba.
5. _ _ _
Kwalliya na gidan duniya dandanon shi mai zaki amma tsami ne asali.
6.
_ _ _ Duk wanda ya bi son ranshi kuma yayi girman kai haqiqa yayi barna.
7. "Lallai na ga kawuna sun nuna"
----Hajjaj bn Yusuf
____________________mp3, 6.5mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQVkRfZ1JjcHdOeWs/view?usp=drivesdk
■
0036
10/01/2017
Karatun Lugha
___Darusa_______
1._ _ _
Lallai rai na wanda ke umurnina da mummunan aiki be wa'azantu ba da mai gargadi na furfura mai tsufa saboda jahilcinsa.
2. _ _ _
Duk wasu ayyuka na alkhairi taken manzon Allah ne tsawon zamani.
3. _ _ _
Mashi ya damfàre su.....
4. _ _ _
Duk wanda zamani bai mishi wa'azi ba to malami bai isa ya yi masa wa'azi ba.
5. _ _ _
Kwalliya na gidan duniya dandanon shi mai zaki amma tsami ne asali.
6. _ _ _
Duk wanda ya bi son ranshi kuma yayi girman kai haqiqa yayi barna.
7. _ _ _
"Lallai na ga kawuna sun nuna"
----Hajjaj bn Yusuf
____________________mp3, 6.5mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQVkRfZ1JjcHdOeWs/view?usp=drivesdk
■
0037
16/01/2017
___Darusa_______
1. _ _ _
Littafin layya da ragon suna da farauta da yanke-yanke.
>> hukunce-hukuncen layya:
▪layya sunnah ne.
▪ana yi da dabbobin gida.
+ tinkiya_daga wata shida (6) ko sama.
+ rago me qaramin qira_daga shekaru biyu (2).
+ sanuwa_daga shekaru uku (3)
+ rakumi_daga shekar shida (6)
▪ba'a yanka da dare.
▪ana nisantar aibi;
- dabba makaho ko mai ido daya.
- rashin lafiya.
- da qeqashewa.
- da karyewan qaho mai jini.
2. _ _ _
Mai fuska biyu baya kasancewa mai daraja a wajen Allah.
3. _ _ _
Misali akan maf'ul.
I. Mace ta mutu ta bar
▪Miji ▪uwa ▪yan uwa biyu (2) li-abbai ▪affun li-abb ▪dan uawa wanda babu shi.
____________________mp3, 6.6mb
■
0038
17/01/2017
Karatun Lugha
___Darusa_________
1. _ _ _
Fasali gamed da harufofi na qari.
2. _ _ _
An ruwaito da tsantsan kasara da ishmami na domma.
3. Addu'a'u Billa'an - shar'antuwan yin addu'a ga masu mulki (addu'a na shiriya)
4. _ _ _
Kada natsuwan malam ya ruwde ka (kada ka dauka malam rago ne).
5._ _ _
Nasaba da Fataha.
___________________mp3, 7.1mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQWW1QTU5kMHNBNzg/view?usp=drivesdk
■
0039
18/01/2017
Littafan Danfodio
___Darusa__________
1. _ _ _
Tabbatar da zuciyar manzon Allah ta hanyar sauqar da ayoyin lallashi da ayoyin da suke hani daga baqin ciki (akan abun da kafirai ke aikatawa a kansa na cutarwa).
2. Ahkamu Janaa'iz - Aikawa da fallayen takarda (wasiqa) a qabarin annabi.
3. _ _ _
Daga cikinsu (a qasar hausa) akwai wanda yake cewa shi musulmi ne kuma yana da'awan sanin gaibi.
4. _ _ _
Ya yan uwa! Kusan cewa gyaruwan al'umma da gyaruwan malamai yake. Bacinsu da bacin malamai yake.
- - ahlul zikiri ba mai dukan qirji bane. Ahlul zikiri shine mai ilimi da taqawa.
5. Ihya'ussunnah - daga cikin hanyan sunnonin manzon Allah daga cikin abun da ya hau kan mata;
□ hani daga saduwa da su(lokutan hayla) da kuma jin dadin abun da ke qasan gyauto.
□ hana sakin mata a kwanakin hayla.
□ bayan hayla ta dauki auduga ta sa amisqi ta sanya a wajen hayla(sau uku) don gusar da qarni.
6. _ _ _
Daga cikin abunda mutane suke qirqirowa a cikin babi na taymama.
______________________mp3, 8.2mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQUFBGOWN5dm1Xanc/view?usp=drivesdk
■
040
--------------
Karatun Asuba
____Darusa____________
1._ _ _
Sunayen Khawarij:
Suna na biyu (02) Haruriyya:
ana danganta su da garin Harura(kusa da kuwfa) inda magabatan su suka koma bayan sunyi tawaye daga rundunar Aliyu (ra).
Suna na uku (03) Ash-Shurah:
wato sayar da kansu ga Allah.
Suna na hudu (04) Al-Mariqa:
wato tawaye don sunyi tawaye daga rundunar Aliyu (as).
Suna na biyar (05) Al-muhakkima:
wato masu kai hukunci zuwa ga Allah. Saboda inkarin hukuncin da ka yi wa •abu musal ash'ari, da • amru bn as.
2. _ _ _
Kashedinka daga debe tsammani daga samun karatu.
3. Bulugul Maram ➡ manzo Allah ya ranci ruqumi daga wani mutum sai aka kawo rakuman sadaka....
4. Usulussunnah ➡
"duk wanda ya bar sallah haqiqa ya kafirta"______mazhab Imam Ahmad.
__________________mp3, 11.8mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQWWtfWlI5c0c2a1E/view?usp=drivesdk
0041
19/01/2017
Karatun Alhamis
Sheikh Bashir bn Nuhu
Majalisin Badarawa
1. Almir'ātu Fi Ahkam Dimā'il Mar'atu
▪ haila ya zo mata daf da sallar la'asar amma bata yi sallar azahar ba...
2. Nuwrul Yaqin
▪daga cikin wanda aka cutar da su wajen bin hanyar Allah shine Abubakar Sadiq...
3. Littafi: Matan gameda sauqowan Isa dan Maryam.
▪Littafiin yana bayani akan dawowan annabi isa(as) da hujjoji da suke nuna haka....
4.
_____________11mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQdHQydTFNQmF0LTg/view?usp=drivesdk 0042
25/04/438 . 24/01/2017
Karatun Talata
Sheikh Yahya bn Muhammad
Majalisin Badarawa
1. Jawami'ul Fawa'id Fi Tahsilil ilmil Nafi (P. 32) ➡
▪a cikin duniya akwai dagāwa(ji da kai) guda biyu ta fannin ilimi....
2. _ _ _ ➡
▪babin kwadaitarwa akan kushu'i a cikin sallah....
3. Riyadussalihin ➡
▪hadithi na shida(6) an karbo daga AbuHurairah(ra) Manzon Allah(saw) ya ce: "kowane gaba akwai sadaka akanta...."
4. Adduraru Bahiyya ➡
▪muhimmancin karatun firak, wawaita tunanin musulmi zuwa ga halin da suke ciki na rauni da rashin ci gaba da kuma tsoron abunda ya risqe su na asara da rarrabuwa zuwa ga qungiyoyi....
Tambayoyi
_____________13mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQb21rUFR6bUV1VGs/view?usp=drivesdk 0043
31/02/2017 .
Karatun Alhamis
Sheikh Bashir bn Nuhu
Majalisin Badarawa
1. Almir'ātu Fi Ahkam Dimā'il Mar'atu ➡
▪Jinin isti'aza: shine gudanan jini daga farjin mace (wanda ba lokacinsa ba) daga wata jijiya. "Zungura ce daga zungurar shaidan" inji manzon Allah(saw)....
2. _ _ _ ➡
Babin fadin Allah ta'ala "ashe baka ga ▪wanda suke riya cewa sunyi imani da abunda aka sauqar da shi gare ka da abunda aka sauqar dashi gabanin ka, suna buqatan su kai hukunci zuwa ga dagutu alhalin an umurce su da su kafirce masa.....
3. Albidaya fi ilmil Mawarith ➡
▪na uku, dan uwa shaqiqi ana shamakance shi da mutane hudu;
uba kaka da' jiyka.
Classwork 1 - 3
...
4. UmdatulAhkam ➡
▪an karbo daga Jabir bn Abdullahi: manzon Allah(saw) ya hana cinikin yabonya da cinikin abinci a jikin zangarniya shi da cinikin danye da busashshe.....
Tambayoyi
▪yaya hukuncin sallah da madubin ido?
_____________8mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQSzJOV2NzRFhRNjg/view?usp=drivesdk 0044
02/02/1438 . 31/01/2017
Karatun Talata
Sheikh Yahya bn Muhammad
Majalisin Badarawa
1. Jawami'ul Fawa'id Fi Tahsilil ilmil Nafi (P. 33) ➡
▪muawwiqi na bakwai(07): Tsarkake rai; watau mutum yake ganin shi mai tsarki ne akan sauran mutane, da son yabo...
2. Kashfushubuhat fi masa'ilil ahad wal jihad ➡
▪yayin da ya kasance makoma na hukuncin kafirtawa yana ga Allah da manzonsa. Baya halatta mu kafirta, sai wanda Qur'ani da hadithi yayi nuni ga haka. Ba'a aiki da zato...
3. Usulul Fiqh ➡
▪na uku kayi tasarrufi cikin mulkin sa don ya cutar da mutane....
4. Tuhfatussaniyya ➡
▪mubtada kashi biyu ne; bayyananne(zahiri) da boyayye(damiri).....
Tambayoyi
_____________13mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQVW5FZ0tRakxzeWs/view?usp=drivesdk 0045
02/02/2017
Karatun Alhamis
Sheikh Bashir bn Nuhu
Majalisin Badarawa
1. Almir'ātu Fi Ahkam Dimā'il Mar'atu ➡
▪Jinin isti'aza: wanda ta saba yin al'ada amma ba ta iya banbance
2. _ _ _ ➡
▪Tambaya ta uku; shin ya kamata mata su tsawatar da mutane daga littafan Sa'idul Kutub? In tana da dalibai mata ta tsawatar da su akan littafan Sa'idul Kutub....
▪Sa'idul Kutub yana da aqida na shia'a/Khawarij, Mu'utazila/Murji'i/Suwfi.
____mawridul azaba....sheikh Albani yayi takhriji.
▪ Sa'idul Kutub yayi zantuka marassa kyau ga annabi Musa(as).....sheikh Rabih yayi raddi.
3. _ _ _ ➡
▪babi da zai magana akan azumi; azumin watan ramadana farilla ne, ana daukan azumi da ganin jinjirin wata, ana ajiye azumi da ganin jinjirin wata.....
4. Ibn Rushud ➡
▪ya zo: a inda mutum yayi watsi da niyarshi daya dauka na alwala, bai warware alwalarshi ba.....
Tambayoyi
_______________10mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQNG5GZ1lGdHpwWjg/view?usp=drivesdk 0046
09/j ula/ 1438 . 07/02/2017
Karatun Talata
Sheikh Yahya bn Muhammad
Majalisin Badarawa
1. Jawami'ul Fawa'id Fi Tahsilil ilmil Nafi (P. 33) ➡
▪Allah ta'ala Ya zargi ahlul kitab "shin baku ganin wadanda suke tsarkake kawunan su, Allah ta'ala Shi ke tsarkake wanda ya so kuma ba'a zaluntarshi ko kwallon dabino.....
2. Addu'a'u Billa'an ➡
▪matsala ta bakwai(07); bayyanar da qiyama ga kafirai gwargwadon yadda shari'a ya tabbatar.....
3. Manhaju Ahlus-sunnah wal jama'a ➡
▪raddi ga ma'abota son rai(yan bidi'a); wani babi ne mai girma daga cikin babi na jihadi.....
4. _ _ _ ➡
▪daga cikin shuhubobi wanda Mu'utazila suka dogara a kai da kuma wanda suka tafi akan maganar su "Allah ya cewa Musa ba zaka taba gani na ba" suka ce wannan dalili ne cewa Allah ba za'a ganshi a gobe qiyama ba ....
5. Masa'ilil Jahiliyyah ➡
▪yana daga cikin matsala na jahiliyyah, shine riqo da rabuwa da barin hadin kai....
Tambayoyi
_____________12mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQLVhFMWpxYWR1alE/view?usp=drivesdk 0047
09/02/2017
Karatun
Sheikh
Majalisin Badarawa
1. Almir'ātu Fi Ahkam Dimā'il Mar'atu ➡
▪me jinin isti'aza wacce ta fara haila amma bata iya banbance jinin isti'aza da haila...
2. Mu'amalatul Ahkam ➡
▪ta ambaci sashen mukhalafat wanda suka abku daga sashe talakawa ga haqqin shugaba.....
L
3. Al fatawa Al muhimma ➡
▪su wa nene jama'atu Tabliq, wace manhaji suke tafiya akai.....
4. Musdala'il Hadith ➡
▪Hadithi Gharibi: mafi shaharan littaffai da ake yin rubutu kan hadithi gharibi....
Tambayoyi
Liman yana sallah da najasa a jikin tufafinda?
_____________8mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQZkJsNS1yS09wU3M/view?usp=drivesdk 0048
16/j ula/1438date
Karatun Talata
Sheikh Yahya bn Muhammad
Majalisin Badarawa
1. Jawami'ul Fawa'id Fi Tahsilil ilmil Nafi (P. 34) ➡
▪imamul minziri ya kawo a cikin littafinsa watau 'tsoratarwa ga da'awar tsarkakan kai da hatsarinsa.....
2. Ibn Ashir ➡
▪siffar zama a sallah.....
3. _ _ _
▪an karbo daga A'isha(ra): na tambaye manzon Allah(saw) game da waiwaye a cikin sallah sai ya ce: "fisgewa ne da fisgewan shedan wanda yake wa sallar bawa"....
4. Tauhidi.
Tambayoyi
____________11mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQVHJDdXZ1Yk10Tkk/view?usp=drivesdk 0049
16/02/2017 .
Karatun Alhamis
Sheikh Bashir bn Nuhu
Majalisin Badarawa
1. Almir'ātu Fi Ahkam Dimā'il Mar'atu ➡
▪mace mai jinin isti'aza wace ta manta al'adanta da adadin kwanaki, kuma ba ta iya banbance jinanai....
2. Nuwrul Yaqin ➡
▪lokacin da kafiran quraishawa suka ga wannan cutarwa da suke wa musulmai bai amfane su ba, musulman da suke cutarwa imaninsu ma qaruwa yayi....
3. _ _ _ ➡
▪Farkon wanda aka sani daga gare shi, inkarin sunayen Allah da Siffofin Allah
Tambayoyi
Mutum ne ya rasu, ya bar N700,000 da matan aure biyu da ya'ya' maza(6), mata(2). Ya za'a raba gado?
_____________10mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQNTd5WHl2VU1tSmM/view?usp=drivesdk 0050
23/j ula/1438
Karatun Talata
Sheikh Yahya bn Muhammad
Majalisin Badarawa
1. Jawami'ul Fawa'id Fi Tahsilil ilmil Nafi
▪ya kamata maabocin ilimi kada ya qasqantar da kanshi da kwadayi a cikin abunda ba'a kwadayin sa. Duk abun da ya qinshi qasqanci ga ilimi ya kamata ya kyamace shi...
2. Riyadussalihin (hadithi na. 7) ➡
▪ Abu Hurairah: manzon Allah ya ce: "duk mutumin da yayi sammako zuwa masallaci Allah zai tanada masa wani liyafa a gidan aljannah".....
3. Adduraru Bahiyya ➡
▪muhimmancin karatun firak: banbance - banbancen qungiyoyi na bakwai (7); sadar da alaqa da al'ummah na yanzu da na da. Misali mutanen da suka ce Alkur'ani halitta ne, shin haka sahabbai suka ce? ......
4. Kashfushubuhat ➡
▪wannan hukunci kamar waninsa ne cikin hukunce - hukunce, wanda basa cika sai da samuwan sababinsu da sharudansu....
Tambayoyi
_____________11mb
https://drive.google.com/file/d/0ByZVip6zcbuQZk9QSzdidVNrSXM/view?usp=drivesdk
Comments
Post a Comment